Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Barcelona: Messi ke samar da kaso uku na kudaden shiga – Laporta

Published

on

‘Yan takarar shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Joan Laporta da Victor Font sun ce hakika ya kamata albashin Lionel Messi ya wuce yadda ake biyanshi a yanzu duba da irin makudan kudaden shiga da yake samawa kungiyar.

‘Yan takarar sun bayyana hakan ne yayin tattaunawa da wata jarida ta kasar Spain kan batun kwantiragin sa.

Sun kuma ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa Messi yana samawa kungiyar kaso uku a jimillar kudaden shiga da kungiyar ke samu.

A yanzu haka dai kwantiragin Messi da Barcelona zai kare ne a karshen wannan kakar wasan da muke ciki ta 2021.

Laporta da Font sun kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin Messi ya ci gaba da zama a kungiyar matukar suka samu shugabancin kungiyar a zaben da za a gudanar ranar 7 ga watan Maris mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!