Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FIFA: ‘Yan wasa 8 za su buga wa Najeriya wasa

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa ‘yan wasan Najeriya guda takwas da aka haifa a kasashen waje damar fara buga wa Najeriya wasanni.

‘Yan wasan sun hadar da Ovie Ejaria dake a kungiyar kwallon kafa ta Reading da Ademola Lookman dan wasan gaba a Fulham da Jordan Torunarigha daga kungiyar Hertha ta kasar Jamus da Nathan Tella dake a Southampton.

Sauran su ne: Tosin Adarabioyo shima dake a Fulham da Noni Madueke a kungiyar PSV da Sheyi Ojo dake a Cardiff City sai kuma dan wasan gaban kungiyar Chelsea da a yanzu haka yake a Cercle Brugge a matsayin aro Ike Ugbo.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya tabbatar da cewa FIFA ta sahalewa Ovie Ejaria wanda aka haifa a kasar Ingila ya fara buga wa Najeriya wasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!