Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Barcelona za ta iya doke Bayern Munich – Xavi

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Xavi Hernendez ya ce kungiyar nada kwarin gwiwa a kan wasan da zasu buga a daren yau a gasar cin kofin zakarun turai Champions League da Bayern Munich.

Barcelona dai na bukatar lallai sai ta samu nasara a kan Bayern Munich domin kaiwa zagaye na gaba, amma sai dai Xavi ya ce ba za su wani takura kansu a wasan ba.

Tawagar ta birnin Catalan na iya fuskantar koma baya muddin ta gaza kaiwa matakin gaba a gasar.

“Lamarin wasan yau na hannun mu, domin zamuyi abin da ya da ce domin samun nasara, kuma da sannu bayan kammala wasan zakuga me zai faru,”

“Kuma zamu kasance masu juriya da kuma bin wasan cikin nutsuwa da taka tsan-tsan, wanda hakan zai bamu damar samun nasara a hannun Bayern Munich,” a cewar Xavi yayin ganawarsa da manema labarai gabannin wasan.

Xavi ya kuma kara da cewa sarai kungiyarsa ba za ta yi sake da Bayern Munich ba kasan cewa har filin wasa Allianz Arena za su ziyarta domin buga wasan.

Barcelona dai na mataki na biyu a rukunin E da maki 7, yayin da Bayern Munich ke a mataki na farko da maki 15 da tuni ta kai zagaye na 16.

Haka zalika Benfica ce a mataki na uku da maki 5 da itace kungiyar da za suyi takara da Barcelona wajen samun gurbin kungiyoyi 16 a gasar ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!