Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Barista Hussaina Aliyu:Matan da mazajensu suka rasu na fama da matsalolin ta fannin ‘yan uwan miji

Published

on

Tsohuwar shugabar kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa reshen Kano Barista Husaina Aliyu Ibrahim, ta ce da yawa daga cikin matan da mazajensu suka mutu suna fama da matsaloli ta fannin ‘yan uwan wadanda suka rasu musamman wajen rabon gado.

Barista Husaina Aliyu Ibrahim, ta bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘Mu leka Mu Gano’ na musamman na nan Freedom Rediyo a daren jiya Lahadi, wanda ya mayar da hankali kan irin matsalolin da zawarawan da mazansu suka rasu suke fuskanta.

Ta ce akwai mutane da dama da suke jefa irin wadannan mata cikin mawuyacin hali musamman ma idan wanda ya mutun ya bar kadarori, sai su fake da kulawa ‘ya’yan mamacin abinda aka bar mu su.

Haka kuma ta kara da cewa akwai wasu daga cikin irin wadannan mata da ko da an yi yunkurin taimaka musu sai su ce sun bari har zuwa ranar gobe kiyama, wanda hakan bai kamata ba.

Lauyar ta kuma ce kungiyarsu na taimakawa irin wadannan mata tare da kwato mu su hakkokin na su a kyauta, a yunkurinsu na magance irin wadannan matsaloli.

Barista Husaina Aliyu Ibrahim, ta bukaci duk matan da ke fuskantar irin wannan matsala da su garzaya ofishinsu da ke ofishin Inuwar jama’ar Kano da ke kusa da ofishin hukumar Road Safety a nan Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!