Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Yadda annubar Corona ta kassara kananan ‘yan kasuwa a Kano

Published

on

Har yanzu masu kananan sana’oi a nan jihar Kano na cigaba da kokawa dangane da irin yadda bullar annobar cutar corona ta durkusar musu da tattalin arzikin kasuwancin su musamman a zaman kulle da aka shafe tsahon watanni a cikin sa.

Irin wadannan ‘yan kasuwa sunyi ikarin cewa bayan wahalar rayuwa da suke fuskanta da iyalansu a yanzu na rashin ciniki da kuma matsalar tashin farashin kayayyaki matsalar cutar Covid-19 ta sanya mafi yawa daga cikin ‘yan kasuwar sun rasa jarikansu.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa daya ziyarci karamar hukumar Bebeji ya rawaito cewa  matsalolin da wasu daga cikin ‘yan kasuwa a karamar hukumar ke fuskanta ya yi kamari.

Wadannan ‘yan kasuwa sun shaida mana cewa daga lokacin da annobar cutar Corona virus ta bulla a nan Kano aka kuma sanya dokar zaman gida na kulle masu kananan sana’oi suka fara dan dana kudar su wanda hakan yasa jarinsu ya fada cikin mawuyacin hali tare da tasamma durkushewa.

Sani Ibrahim mai lakabin mai ‘yar sana’ar yara dake sayarda soyayyar Doya a Garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji wanda ya kashe sama da shekaru goma sha shida yana sana’ar yace:

“Annobar cutar Corona virus tayi masa matukar illa a harkar kasuwancin a yanzu wanda hakan yasa bashida jari sosai kamar yadda yake dashi a baya ga kuma matsalar da ake fama da ita a yanzu na rashin ciniki sosai. Yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta kawo musu dauki kasan cewar cutar corona tayi musu illa “

Haka zalika shima wani dattijo mai suna Alhaji Uba Tiga dake gudanarda sana’ar kayan kanti wanda ya kashe sama da shekaru arba’in yana gudanarda sana’ar inada yace:

“Cinikin da sukeyi a baya ko rabinsa basayi a yanzu wanda hakan yasa jarinsa ya sami matsala sosai musamman a yanzu kasan cewar abaya jarinsa ya dara sama da naira dubu dari da takwas amma yanzu jarin nasa bai gaza dubu dari biyar ba domin duk yayi amfani da kudin wajen ciyarda iyali a lokacin zaman kulle na Lockdown”

Daya daga cikin masu gudanarda sana’ar sayarda kifi a kwanar Bagauda wato ‘yan Kifi yace:

“Sunyi matukar tafka asara bayaga rasa jarin su da sukayi saboda corona musamman a harkokin suna’ar su ta sayarda kifi da kaji a kasuwar baki daya, wanda kuma a yanzu haka kasuwar ke dauke da matasa sama da dubu guda amma mafi yawa daga cikin su basu da jari a halin yanzu “

‘Yan kasuwar a nan Kano dai na cigaba da kira ga jama’a musamman gwamnati da a kawo musu dauki musamman wadanda suka gamu da iftila’in karyewar jarin su sakamakon bullar annobar cutar Corona a Kano da akasha fama da ita wanda ta jefa rayuwar su da ta iyalansu cikin matsala a yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!