Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Bashin da ake bin Nigeriya ya haura tiriliyan 49 DMO

Published

on

Ofishin Kula da Basusuka na Nijeriya DMO ya ce, jimillar bashin da ake bin kasa a yanzu ya kai Dala biliyan 103.3, kwatankwacin Naira tiriliyan 49 da biliyan ɗari 8 zuwa ranar 21 ga watan Maris din da ya gabata.

 

Ofishin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a.

 

sanarwar ta bayyana cewa bashin ya hada da kudaden da ake bin jihohi da gwamnatin tarayya, sai dai ban da wanda babban bankin CBN ke bin gwamnatin.

 

Sanarwar ta kuma ce, wancan adadi na Naira tiriliyan 49 da biliyan 800, bai kunshi Naira tirliyan 22 da biliyan 7 din da CBN ke bin Gwamnatin Tarayya ba, wanda Mlmajalisar dokoki ta sahale wa gwamntin ciyowa a watan Mayun da ya gabata, wanda za a saka shi a jerin basussuka na cikin gida cikin wannan watan da muke ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito

 

*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!