Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bauren kano-Horas da matasa sana’o’i zai rage aikata laifuuka

Published

on

Bauran Kano Hakimin Rogo Alhaji Muhammad Maharaz,ya ce bunkasa matasa tare da Samar musu aiyyuka yi musamman ma na hannu a sana’o’i daban -daban da suka kware ko koya musu zai taimaka matuka don kaucewa aikata munanan laifuka a hannu daya kuma tare da kawar da zaman kashe wando gare su kasancewar su kashin bayan gina duk wata al’umma mai tasowa .

Muhammad Maharaz ,ya bayyana haka ne a taron wata -wata na ilmantar da matasa gwagwarmayar rayuwar mashahuran mutane mai taken ‘Inspiring leadership interactive session ILERISda cibiyar bunkasa fasahar sadarwar zamani da cigaban al’umma CITAD , ke shiryawa duk karshen wata a ofishin ta don zaburar da matasa.
Bauran Kano ,ya kara dacewa dukkan kasashen da suka cigaba Nada manufofi na musamman akan matasan kasashen da kuma tsarin da ake so su taso dashi wanda zai amfani kasashen nasu dasu kansu matasan tare da kai kasashen ga cigaban da suka tunkara ba wai yin biris da su ba.

A na sa jawabin babban jami’in yada labarai da bincike na cibiyar ta CITAD,Hamza Ibrahim ,ya ce manufar taron shi ne tara matasa tare da fadakar da su don fuskantar rayuwa tare da daukar darusan da suke cikinta don tunkarar kalubale da kuma warware shi.

Taron ya samu halartar dimbin jama’a da dama da suka hada da dalibai,masana daban -daban kungiyoyin gwagwarmaya masu zaman Kansu, an kuma karkare taron da yin tambayoyi da amsoshi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!