Labarai
Bayan biyan bashi, an mayar da wutar ofisoshin jakadancin Najeriya

Rahotonni sun tabbatar da cewar an dawo da wutar lantarki a ofishin Jakadancin Najeriya a Afrika ta Kudu bayan katse ta, ta dalilin tulin bashi.
Babban Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Pretoria, ne ya tabbatar da hakan bayan ofishin ya biya bashin kudaden da ake bin sa.
Hukumomin na birnin Pretoria sun ce an katse lantarkin ne a ranar Litinin a matsayin matakin tilasta bin doka, sakamakon rashin biyan kudade da sauran hidimomin da ofishin jakadancin Pretoria ke bi na dogon lokaci.
Bayan biyan bashin, an maido da lantarkin ga ofishin jakadancin.
You must be logged in to post a comment Login