Labarai
Za a yi wa kudin tsarin mulkin Nijeriya bayan Sallah
Majalisar dattijai ta ce za’a yi wa kudin tsarin mulkin kasar nan garanbawul da zarar an dawo daga hutun sallah.
Tuni shiri yayi nisa na yin gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar nan, da za a ci gaba da gudanarwa jim kadan bayan kammala hutun Sallar Layya.
Sanata Ovie Omo-Agege wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattajai ne ya bayyana hakan, yayin da ya karbi bakuncin wasu kungiyoyin ci gaban mata da wanzuwar ilmi a birnin tarayya Abuja.
Ya ce kwamitin da za su gudanar da aikin za su fara ka’in da na’in bayan hutun Sallar layya da za a yi a makon nan.
Sanatan ya jaddada cewa, shakka babu yayin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, za a sanya dokoki da za su baiwa mata da yara kariyar da ta kamace su a Najeriya.
Ovie Omo-Agege ya kuma kara da cewa, duba da goyon bayan da suka samu daga fadar shugaban kasa, yana da cikakken kwarin gwiwa cewar kudurin zai samu kulawar da ta dace daga sauran bangarori masu ruwa da tsaki
You must be logged in to post a comment Login