Labarai
Bayar da belin Abba Kyari’ ba yana nufin kotu ta sallame shi ba ne- Barista ‘Dan tani
A yau Alhamis babbar kotu Mai cikakken Iko a Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a James Omotoso ta bada belin Abba Kyari bayan watanni goma sha takwas.
Daya daga cikin lauyoyin da suka tsayawa Abba Kyarin, Barista Hamza Nuhu Dan Tani ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da Freedom Radio.
Barista Hamza ya bayyana cewa ‘kotun ta bayar da belin nasa ne duba da cewa laifi da ake zargin Abba Kyari ba babban laifi bane’.
‘Haka zalika ya bayyana cewa ko a lokacin da aka kai hari gidan Yari na kuje Abba Kyari bai gudu ba, wanda ya zama babbar shaidar da kotu tayi amfani dashi wajen bayar da belin Abba Kyari’.
‘Haka zalika an duba ire-iren hidimar da Abba Kyari yayiwa kasa, wanda taga hakan ya taimaka wajen bada belin nasa’.
‘Sai dai kuma hakana hakan ba Yana nufin Abba Kyari zai iya tafiya wajen iyalansa ba, biyo bayan wata tuhuma da wata babbar kotu ta gabatar dashi, Inda NDLEA take tuhumar Abba Kyarin, har sai bayan an gama wannan shari’ar, ko an bada beli, ko kuma a Kori wannan karar.
You must be logged in to post a comment Login