Labaran Wasanni
Bayern ta sallami Barcelona daga kofin turai bayan yi mata Ruwan kwallaye
Kungiyar Kwallon kafa ta Bayern Munich ta tsallaka zuwa zagayen kusa kusa da na karshe ‘Semi final’ a gasar kofin Zakarun Turai bayan ragargaza Barcelona da ci 8 da 2 da tayi a daren yau.
Tun da fari dan wasa Thomas Muller ya saka tawagar ta Munich a gaba a minti 4 da fara wasan bayan samun taimako daga Lewondowski, kafin daga bisani Barcelona ta rama a minti na 7, ta hannun dan wasa Alaba da ya zura Kwallo a gidan su ‘Own goal’.
Ivan Perisic da Serge Gnabry da Thomas Muller sun kara kwallaye uku da suka baiwa kungiyar ta Munich damar kafa sabon tarihin zura kwallaye masu yawa cikin kankanin lokaci na farkon rabin lokaci a gasar, kasa da minti 31, a cikin mintuna na 22 da 28 sai 31.
Labarai masu Alaka.
Kaka-tsara-kaka: Barcelona ko Bayern Munich, wa zai samu nasara a wasan yau?
Bayern ta lashe gasar Bundesliga karo na 8 a Jere
Bayan dawowa hutun Rabin lokaci , dan wasan Barcelona Luis Suarez ya rage Kwallo daya kana ta biyu ga tawagar sa a minti na 57, sai dai jim kadan Bayern ta sake sukuwa da zamiya da kwallaye biyu a minti na 63 da 82 ta hannun Joshua Kimmich da Lewondowski , bayan samun taimako daga ‘yan wasa Davies da Coutinho.
Coutinho wanda ya shigo wasan a minti na 75 bayan dawowa hutun rabin lokaci ,kana kuma dan wasan Barcelona dake a matsayin aro , ya karawa kungiyar sa ta asali kunan zuciya bayan da ya zura kwallaye biyu a minti na 85 da 89 bayan samun taimakon ‘yan wasa Muller da Hernandez , wanda hakan ya kawo adadin Kwallon zuwa 08 ga Munich Barcelona na da 02.
Wannan shi ne karo na farko da Barcelona ta kwashi ruwan kwallaye har sama da shi da , tun bayan shekaru 69, a shekarar 1951 , bayan da Espanyol ta lallasa ta daci 6 da nema a was an da suka fafata a gasar La Liga.
Yanzu Bayern Munich na dakon Lyon ko Manchester City ga duk kungiyar data samu nasara a wasan da zasu fafata gobe Asabar.
You must be logged in to post a comment Login