Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bazamu bari zanga-zanga ta lalata zaman Lafiyar Kano ba: KPC

Published

on

Kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano KPC ya bukaci al’umma dasu sanya zaman lafiyar jihar a gaba da komai.

Shugaban kwamitin Ibrahim Abdu Wayya, ne ya bayyana hakan yayin taron da kwamitin ya gudanar da matasa kan shirye-shiryen da wasu daga cikin al’ummar kasar nan keyi na zanga-zanga kan tsadar rayuwa a gobe Alhamis 01 ga watan Augustan shekarar 2024.

Ya ce duk da cewa zanga-zanga ta halasta a kundin tsarin mulkin kasa amma yana da kyau al’ummar jihar Kano musamman matasa su yi karatun ta nutsu don ganin ba ayi amfani dasu wajen ruguza kasar nan ba.

Ya ce hakika al’umma suna cikin wahala a kasar nan sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da rashin imani na shugabanin a kasar nan.

Ibrahim Abdu Wayya, ya kara da cewa har yanzu ba a san suwaye suka shirya zanga-zangar ko manufar yinta ba wanda hakan ke kara jefa shakku a zu katan al’umma.

A don haka ya bukaci matasa da kada su bari ayi amfani dasu da sunan zanga-zanga wajen lalata dukiyar mutane.

Ya ce dole ne sai al’umma ta zama ta gari sannan za a samu cigaban kasa.

Ya Kuma nemi matasa da su kaucewa tada hankali ko goyan bayan tayar da fitina a jihar Kano da sunan zanga-zanga.

Daya daga cikin matasan da suka halarci taron, Kamilu Adakawa, ya ce ba zasu shiga zanga-zangar da za ayi ba, inda ya bukaci gwamnan Kano da ta shige musu gaba wajen biya musu bukatun su.

Ya ce a baya an yi musu alkawari da dama wanda hakan yasa suka dena aikata laifukan da suke yi sai dai har yanzu ba a cika musu alkawarin ba.

Kamilu Adakawa, ya kara da cewa da yawan su na fama da yunwa da rashin aikin yi kuma shine babban dalilin da yasa suka kudiri aniyar shiga zanga-zangar a baya.

Sai dai ya ce bisa alkawarin da gwamna Abba Kabir Yusuf yayi na mika bukatun su ga gwamnatin tarayya tasa suka janye daga shiga zanga-zangar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!