Labarai
Bazoum ya jinjinawa hukumar wanazar da zaman lafiya bisa gudunmawa da ta ke bayar a ƙasar ta Nijar
Hukumar Haute Autorité pour la Consolidation de la Paix mai wanzar da zaman lafiya ta Nijar, ta gudanar wani taro da wakilan ƙabilun jihohin Agadas da Tawa.
Taron da ya mayar da hanakali kan yadda suka taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin da a baya ya fuskanci rikicin ƴan tawaye.
Shugaban ƙasar Bazoum Mohammed ne ya jagoranci zaman a garin Ingal na jihar ta Agadas.
Da ya ke jawabi yayin taron shugaban hukumar Janar Abu Tarka, ya ce sun shirya wannan taron ga ‘yan tawayen da suka tuba don kara tabbatar da tsaro a yankunan.
Bayan sauraran jawabai daga shugabannin yankunan Shugaban kasa Bazoum, ya jinjina musu bisa kokarin da suke na wanzar da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login