Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nijar

Ƴan adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Nijar

Published

on

Bayan da hukumar zaben jamhuriyar Nijar CENI ta ayyana Malam Bazoum Muhammed a matsayin wanda ya lashe zaben jamhuriyar Nijar da kuri’u sama da miliyan biyu da rabi, rahotanni sun ce tarzoma ta barke a wasu daga cikin jihohin kasar.

A ranar lahadin da ta gabata ne dai aka gudanar da zaben raba gardama, wanda kuma ya baiwa Bazoum din damar lashe zaben da kaso hamsin da biyar cikin dari.

Da yake karanto sakamakon zaben mai shari’a Maitre Issa Gasounni ya ce samun sama da kaso hamsin cikin 100 na kuri’un da aka kada shine ya ke tabbatar da cewa mutum ya lashe zaben.

labarai masu alaka:

Nijar: Bazoum ya kama hanyar lashe zaɓe

Taron ECOWAS : Buhari zai gana da takwarorin sa a Jamhuriyyar Nijar

Tuni dai magoya bayan Bazoum Muhammed suka fara nuna farincikin su game da wannan zaben, a yayin da magoya bayan Muhamman Ousumane ke cewa basu amince da sakamakon ba, tare da fantsama cikin gari da fara kone-kone.

Da yake jawabi kakakin kwamitin yakin neman zaben Muhamman Ousumane Dr. Sani Abdu y ace basu amina da zaben ba, kuma dama tuni ‘yan jam’iyyar da PNDS tarayya suka sha alwashin yi musu Murdiya, a don haka zasu dauki matakin da ya dace.

Shi kuwa mataimakin shugaban hukumar Zaben ta CENI Dr. Haladuwa Ahmada ya ce wannan sakamakon zabe na wucin gadi ne, kotun koli ce kadai zata tabbatar da wanda ya ci zaben.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!