Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Bazoum ya nemi kotun ECOWAS da tasa sojoji su sake shi

Published

on

Hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum ya shigar da ƙara gaba kotun Ecowas, yana neman kotun ta bayar da umarnin a sake shi daga ɗaurin talalar da sojoji ke yi masa tun bayan hamɓarar da shi.

Lauyan Bazoum Seydou Diagne, ya ce an shigar da ƙarar ne ranar Litinin domin neman sakin Bazoum, tare da mayar da shi kan karagar mulkin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa cikin watan Yuli.

“Muna buƙatar a mayar da Nijar kan tafarkin dimokradiyya ta hanyar sakin Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan karagar mulki, domin ci gaba da mulki har zuwa ƙarshen wa’adinsa”, kamar yadda Seydou Diagne, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Matarsa da ɗansa na daga cikin waɗanda ake yi wa ɗaurin talalar tare da Mohamed Bazoum tun bayan hamɓarar da gwamnatinsa.

Ecowas ta yi barazanar ɗaukar matakin soji don mayar da Bazoum kan karagar mulki, idan duka matakan diflomasiyya suka gaza.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!