Labarai
Benue: Yau za’a binne mutane 72 da suka mutu ranar 1 ga Junairun wannan shekara
Gwamnatin jihar Benue ta ce a yau Alhamis za ta yi bikin binne mutane 72 wadanda suka mutu jihar Benue ranar daya ga watan janairun wannan shekara da ake zargin Fulani makiyaya sun kashe.
Maharan dai da har yanzu ba a kai ga tantance su ba da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari wasu kauyuka ne guda biyar a karamar hukumar Logo da ke jihar Benue a lokacin da ake bikin Sabuwar shekara.
A jiya laraba ne Gwamna Samuel Ortom ya sanar da bikin binne wadanda suka rasun yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudan a garin Markurdi, taron da ya maida hankali akan matsalar tsaro a jihar da lalubo hanyar magance shi.
Gwamna Ortom wanda ya shirya taron adduar binne mamatan ya ce za a ci gaba da tuna mamatan saboda sadaukar da rayukan su da sukayi domin kare manoman jihar ta Benue.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su nuna da’a yayin bikin binne mamatan, inda kuma ya bukaci al’ummar jihar da ka da su sake yunkurin kai hari akan kowace irin al’umma.
Gwamnan ya kuma sha alwashin cewar gwamnati za ta zakulo wadanda suka yi aika aikar inda ku ma ya ce gwamnatin za ta hada hannu da jami’an tsaro wajen ganin an magance matsalar