Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Benzema Ya Lashe Kyautar Ballon D’or A Karon Farko

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Faransa Karim Benzema, ya lashe kambun gwarzon dan wasan Duniya bangaren maza na shekarar 2022, yayinda ‘yar wasan tsakiya ta kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Spaniya Alexia Putellas, ta lashe kambun a bangaren mata.

Benzema mai shekaru 34 ya zura kwallaye 44 a wasanni 46, da hakan ya taimakawa Madrid lashe gasar cin kofin zakarun Nahiyar Turai da gasar La Ligar kasar Spaniya a kakar wasanni ta shekarar 2021/2022

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da kasar Senegal ne ya zo na Biyu Sadio Mane, yayinda dan wasan tsakiya na Manchester Citys da tawagar kasar Belgium ya zo na Uku Kevin de Bruyne.

A bara dai dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain da kasar Argentina, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a karo na Bakwai.

An kuma ayyana kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a matsayin kungiya mafi kyawu a Duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!