ilimi
Kungiyar malamai sunyi kira ga gwamnati data kara musu kudin sufuri
Yayin da ake bikin ranar malaman makaranta a yau Alhamis a fadin duniya baki daya, Wanda Majalisar dinki duniya ta ware, don Nuna irin gudunmawar da malaman makarantun ke bayarwa a cikin al’umma, matsalolin da suke fuskanta, tare da lalubo hanyoyin magance su.
A nan Kano kungiyar malaman makaranta ta kasa ta bukaci Gwamnati a matakin jihohi da Tarayya da su Karawa malaman kudin sufurin zuwa makarantun da suke koyarwa sakamakon tsadar man fetur bayan cire tallafi.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Comared Baffa Ibrahim Garko, ya bayyana hakan a wani bangare na bikin ranar malaman da suka gudanar a nan Kano.
Comared Baffa Ibrahim Garko, ya kuma Kara da cewar ‘har yanzu akwai tarin kalubale da Malamai dakuma harkar koyo da koyarwa ke fuskanta wanda ke bukatar a magance su dan inganta rayuwar Malamai da bunkasa Ilimi a fadin jihar Kano da kasa baki daya’.
Ya kuma Kara da cewar ‘a yayin taron na yau Kungiyar ta gudanar da Addu’oi na musamman ga malaman da suka rasu dama wadanda suka jikkata lokacin aikin koyarwa’.
A nasa jawabin shugaban kungiyar kwadago na kasa reshen jihar Kano kwamred Kabiru Inuwa cewa yayi ‘sai da Ilimi ne ko wacce Al’umma take cigaba wanda baya samuwa sai da Gudunmawar Malamai, ta hanyar samun cikakkoyar kulawa daga gwamnati, dama ita kanta al’umma.
Yayin taron dai an gabatar da kasidu da ke nuna irin gudunmawa malaman, da Muhimmancin inganta rayuwarsui da makarantun kansu a matsayin hanyar samar da cigaban kowacce Al’umma.
Rahoton: Abba Isa Muhammad
You must be logged in to post a comment Login