Addini
Bikin Takutaha: Al’umma na ci gaba da bukukuwan zagayowar ranar
A kowacce ranar 19 ga watan Rabiu Auwal al’umma kan fito domin gudanar bikin takutaha da nufin nuna farin cikin su da zagayowar ranar sunan haihuwar annabi Muhammad S.A.W.
A wasu lokutan ma akan yi girke-girke na musamman domin rabawa ƴan uwa da abokan arziƙi.
Bikin Takutaha dai ana gudanar da shi a kowacce shekara a irin wannan rana domin kuwa ranar ta kasance kwanaki bakwai bayan haihuwar manzon tsira annabi muhammad S.A.W.
A Hausance ana kiran ranar da ranar suna don nuna farin ciki da zagoyawar ranar sunan shugaban halitta.
Al’umma dai kan yi sababbin ɗinkuna da girke-girke na musamman sannan wasu kan yi amfani da ranar wajen yin ziyarar ƴan uwa da abokan arziƙi, yayin da wasu kuma ke zuwa hawan dutsen Dala ko na Goron dutse.
Wasu kuwa kan yi amfani da ranar wajen shirya mauludi baya ga sha’irai da kan shirya zagaye su fita suna rera waƙoƙin yabo ga shugaban halitta.
A wani ɓangaren kuwa wasu kan shirya zagayen a kan dawakai ko jakuna ko ko raƙuma yayin da wasu kuma suke yin zagayen a ƙafa.
Muna na tafe da rahotanni kan yadda bukukuwan ke kasancewa a sassa daban-daban a nan Kano har ma da wasu makwabta.
You must be logged in to post a comment Login