Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Takutaha: Abba Gida-gida ya ayyana Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ayyana yau Laraba 4 ga watan Oktobar 2023 a matsayin ranar hutu domin bikin Takurawa don tunawa da Mauludin Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida Baba Halilu Dantiye ya fitar.

Sanarwar ta ruwaito cewa gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan damar wajen yin koyi a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma aiki da su.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ƙara yin addu’a domin samun zaman lafiya da ƙaruwar arziki a Kano da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma yi addu’ar Allah albarkace mu da albarkar noman damina mai albarka a bana da kuma damina mai zuwa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!