Labaran Kano
Bincike: Akwai mahaukata fiye da miliyan 60 a Najeriya
Yayin da ake gudanar da bikin ranar masu fama da lalurar kwakwalwa, wani binciken likitocin kwakwalwa ya gano cewa, akwai masu dauke da lalurar fiye da miliyan 60 a Najeriya.
Wani ma’aikacin jinya a asibitin masu fama da lalurar da ke Dawanau a nan Kano, Malam Yahaya Yusuf ne ya bayyana haka ne ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan ranar masu tabin hankali da duniya da ake gudanarwa kowacce ranar 10 ga watan Oktoba.
Ya ce aakwai hanyoyi da dama da suke janyo lalurar kwakwalwar, wadanda suka hadar da shan miyagun kwayoyi da ta’ammali da tabar Wiwi da cutar damuwa da sauransu.
Shi kuwa wani malami a sashen bada shawarwari da gyaran tarbiyya a kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke nan Kano Dr Bashir Sani, ya bayyana cewa, kebe ranar bikin masu lalurar kwakwalwar musamman yadda taken bikin na bana ya kasance ‘’yadda za a magance matsalar yawan kashe kai’’ wanda ake fama da shi a wannan zamani.
Da yake tsokaci ta cikin shirin, wani kwararre a fannin lalurar kwakwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano, Dr. Usman Muhammad Minjibur ya bayyana wasu hanyoyi dakile kashe kai.
Shi ma wani masani a fannin lalurar kwakwalwa Dr. Ya’u Ahmad Sara, ya bukaci iyaye da su rubanya kokari wajen ganin sun baiwa ‘ya’yansu tarbiyya, domin hakan na kange su daga shiga damuwar da za ta sanya su tunanin gwara su kashe kansu.
Rubutattuka masu alaka:
Sheikh Daurawa ya musanta zargin yin rawa a gidan biki
Za’a sanyawa unguwannin ‘yan gayu na’ura mai amfani da hasken rana
Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu