Labarai
Birnin Abuja na cikin kwanciyar hankali da tsaro- Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa birnin tarayya Abuja na ci gaba da kasancewa lafiya ga ’yan ƙasa da baki, duk da sabon gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya fitar kan ziyartar wuraren soja da na gwamnati a birnin.
Wannan na cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Litinin 23 ga Yuni, 2025.
Ya ce, hukumomin tsaron Najeriya na aiki dare da rana don kare lafiyar jama’a, kuma ko kusa ba a samu wata barazana ba a birnin.
Gwamnatin ta ce, ta fahimci cewa wannan gargadi na Amurka ya samo asali ne daga abubuwan da ke faruwa a duniya baki ɗaya, ba wai wani haɗari na gaggawa a cikin ƙasar ba.
Ta kuma jaddada cewa, babu dalilin fargaba, ta na mai karfafa gwiwar ’yan ƙasa kan su ci gaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, tare da sanya ido da sanar da hukumomi idan aka ga wani abu da ba a saba gani ba.
You must be logged in to post a comment Login