Connect with us

Labarai

Biyan haraji ya zama dole – Saƙon Baffa ga ƴan adaidaita

Published

on

Hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta ce, ya zama tilas ga duk masu baburan adaidaita sahu su riƙa biyan harajin Naira ɗari-ɗari a kullum.

Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa doka ce ta bada umarnin a biya kuɗin ba su ba.

Babu sassauci ga ƴan adaidaitar da ba sa biyan haraji – KAROTA

Ba ma shiga ayyukan wasu hukumomi da niyyar cin zarafin jama’a – KAROTA

Ya ce doka ce ta ce ‘yan adai-daita sahun su biya naira dari-darin, a don haka basu da wani dalili na kin biyan kudin.

Baffa kuma ya ce hukumar ta karota ta shirya tsaf wajen sanya kafar wando guda da masu adai-daita sahun da suka bijirewa biyan kudin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!