Labarai
Biyan kudin fansa na taimakawa yan ta’adda su mallaki makamai – Durumin Iya
Daga: Zainab Aminu Bakori
Masani kan sha’anin tsaro kuma mai bincike a fannin aikata manyan laifuka a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke nan Kano Auwal Bala Durumin Iya ya ce biyan kudin fansa ga masu aikata laifuka na taka rawa wajen bai wa masu aikata laifun mallakar makamai da ma wasu abubuwan da basu da su.
Auwal Bala na bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Redio.
Ya ce, lokaci yayi da hukumomi da kuma al’umma za su daina biyan kudin fansa idan anyi Garkuwa da mutane, saboda biyan kudin fansar ga yan ta’adda kara musu karfin iko na mallakar makamai da kuma kara share fagen ci gaba da ayyukan su.
Auwal Bala ya kuma ce, kamata mutane da jami’an tsaro su rika sauraran kowane irin bayani da wani yazo da shi, musamman idan batun ya shafi harkokin tsaro.
You must be logged in to post a comment Login