Labarai
Boko-Haram: Jiragen ‘Super Tucano’ na daf da isowa Nigeria daga Amurka
Kamfanin kera jiragen yaki na A-29 Super Tucano ya ce, ya kammala aikin kera jirgin farko da Nigeria ta sayo daga garesa.
A cewar kamfanin tuni ya gama aikin kera daya daga cikin jiragen.
A shekarar 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ware dala miliyan dari hudu da sittin da tara da dubu dari hudu don sayo jirgin kirar Super Tucano.
Muhamamdu Buhari a cewar sa, za ayi amfani da jiragen ne wajen kakkabe ayyukan ‘yan tadda.
A cikin wani sakon twitter da kamfanin ya wallafa a yau litinin ya nuna cewa tuni ya kammala aikin kera daya daga cikin jiragen kuma yanzu haka an fara gwajinsa.
A kwanakin baya ne dai, kafin murabus dinsa daga aiki, tsohon babban hafsan sojin sama na kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce, a shekarar dubu biyu da ashirin da daya ake sa ran jiragen za su iso Nigeria.
You must be logged in to post a comment Login