Labarai
Boko Haram: Tattalin arziƙin Arewa maso Gabas ya ragu da kaso 50 cikin 100 – Bankin Duniya
Bankin duniya ya ce, ɓarnar da ƙungiyar Boko Haram ke yi ta janyo durƙushewar tattalin arziƙin yankin arewa maso gabashin ƙasar da kashi 50 cikin 100.
Bankin ya bayyana cewa jihohin Adamawa, Borno da Yobe da ke yankin tafkin Chadi, tattalin arziƙin su ya ragu daga kashi 10 zuwa 14 cikin 100 tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013.
A cewar bankin tattalin arziƙin ya samu raguwa da kashi 50 cikin 100 daga shekarar 2018.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da taron tattauna tattalin arziƙin yankin tafkin Chadi, shugaban sashin kula da tattalin arziƙi na bankin Marco Hernandez ya ce: “A arewacin Najeriya, mun ga kashi 50 ko fiye na yadda ayyukan Boko Haram ya shafi amfanin gona”.
Ya kara da cewa “Ayyukan Boko Haram ba wai a iya wuraren da ake tada kayar baya ba ne kaɗai ke shafa ba, yana kuma shafar sassan da ke makwabtaka da inda ainihin harin ya faru”.
Dailypost
You must be logged in to post a comment Login