Labarai
Borno: An yi jana’izar Yan Sanda 4 da suka rasu sakamakon harin ƴan taʼadda

Rundunar Yan Sandan jihar Borno ta yi jana’izar jami’anta hudu da suka rasu a wani harin da ƴan taʼadda suka kai a karamar hukumar Nganzai.
Rundunar, ta bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da jami’inta na hulda da jama’a ASP Nahum Kenneth Daso ya fitar.
Sanarwar ta bayyana sunayen jami’an da suka rasu da suka hada da Insifekta Samuel Ezekiel, Insifekta Sanusi Mohammed, sai kuma Constable Bitrus Luka da Constable Shaibu Bukar.
Sanarwar ta nuna cewa an gudanar da jana’izar ne a makabartar Kawar Maila da kuma makabartar gidan yari da ke Maiduguri.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Borno, Naziru Abdulmajid tare da wasu manyan jami’ai sun halarci jana’izar.
An gudanar da addu’o’i ga mamatan karkashin jagorancin limamin rundunar, CSP Bukar M. Gajibo da kuma Fasto CSP Theophilus Mutum.
You must be logged in to post a comment Login