Labarai
Borno: Mutane 5 sun rasu sakamakon rushewar gini

Aƙalla mutane biyar ne suka rasu, ciki har da wata uwa da yara huɗu bayan rushewar wani gini a jihar Borno.
Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a unguwar Binta Suga da ke birnin na Maiduguri, inda ya jefa mazauna yankin cikin jimami.
Wani mazaunin unguwar Babagana Usman ya shaida wa BBC cewa ginin ba shi da wani lahani kafin ruftawarsa.
Ya ƙara da cewa an gudanar da jana’izar mamatan a Litinin din makon nan.
Sai dai har zuwa lokacin fitar rahoton, hukumomin yankin ba su ce komai ba a kan wannan batu.
You must be logged in to post a comment Login