Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun wayi gari munga ana gini akan makabarta a Ja’in

Published

on

JA’EEN/MAKABARTA
Al’ummar unguwar Ja’een Yamma sun bukaci hukumomi da su dakatar da wani gini da aka fara yi a cikin tsohuwar makabartar unguwarsu.
Mutanen sun ce, sun wayi gari da ganin ana yin gini cikin tsohuwar makabartar wadda aka dade ba a binne mutane a cikinta.
A zantawarsu da Freedom Radio sun ce sunga ana gini a Wani fili, Wanda makabarta ce, duk da cewa yanzu ba’a binne mamata a cikin ta, amma suna ganin batayi tsufan da za’ayi gini a kanta ba.

 


Freedom Radio ta tuntubbi mai unguwar Ja’een din Yamma Malam Ya’u Wakili, Wanda yace ” ya fita yawon tattaki a unguwarsa ya ga ana gini akan tsohuwar makabartar, bayan kuma ya tambayi mazauna kusa da wurin ne, suke bayyana masa cewa makaranta ce gwamnati take ginawa a wurin, kuma yana tunanin wurin mallakin masu kudi ne, don haka bashi da ta cewa.

 

Wakilanmu da suka ziyarci yankin sun rawaito cewa, sun tarar ana ci gaba da yin ciko a makabartar, tare da yin sabon gini kamar yadda mutanen yankin suka yi korafi.

Rahoton: Wakilai

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!