Labarai
Borno: Yan Sanda sun karyata batun yin Zanga-zanga

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ba gaskiya ba ne rade radin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa za a gudanar da wata zanga zanga a jihar.
Wannan dai na cikin wata sanarwar da jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a yau Juma’a 6 ga Maris muke ciki.
Sanarwar ta ce rundunar na ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana, tare da daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da lafiyar mazauna jihar.
Haka kuma, rundunar ta jan hankalin al’ummar jihar da su guji yada da labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
You must be logged in to post a comment Login