Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Brighton ta casa Manchester United a gasar Firimiya

Published

on

Yunkurin Manchester United na zuwa kofin zakarun turai na ci gaba da samun cikas, sakamakon rashin nasara a hannun Brighton da ci 4-0.

Manchester United dai yanzu haka na mataki na 6 da maki 58 a wasanni 37 da ta buga a kakar wasannin da makwanni suka rage a kamalla.

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Brighton Caicedo da Cucurella da Gross da kuma Trossard ne suka zura kwallaye hudun a ragar United.

A daidai mintina na 14 da 48 da 56 da kuma 59 wasan da aka fafata a filin The American Express Community Stadium.

Yanzu haka dai Manchester United wasa daya ya rage mata a Firimiya a kakar shekarar 2021/2022 inda zata kece raini
Crystal Palace a ranar 22 ga Mayun da muke ciki.

Hakan ke nuni yadda Arsenal da Tottenham suka bata ta zarar makin da zai wahala ta iya samu domin wakiltar kasar Ingila a gasar cin kofin zakarun turai ta kakar wasanni mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!