Connect with us

Labaran Wasanni

Mikel Arteta ya sabunta kwantaraginsa da  Arsenal

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya sabunta kwantaragin shekaru uku da tawagar da ke birnin London.

Dan kasar Spain Mikel Arteta  sabon kwantaraginsa da kungiyar zai kaishi har zuwa shekarar 2025 a filin wasa na  Emirates.

Mai shekara 40 ya dai fara jagorantar tawagar birnin London a watan Disambar 2019 bayan sallamar  Unai Emery.

Dan kasar Spain dai tuni ya fara yunkurin kai tawagar gasar cin kofin zakarun turai bayan tsawon shekaru biyar  da suka shafe ba su je ba.

Yanzu haka dai Arsenal na mataki na hudu da maki 63 a wasanni 34 da wasanni kadan ya rage a kamalla kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!