Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buɗe boda ne kawai zai kawo sauƙin farashin Shinkafa – Muhyi Magaji

Published

on

Hukumar ƙarɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano ta ce ta yi iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta magance ta’azzarar farashin Shinkafa sai dai a wannan karon abin ya ci tura.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan, ta cikin shirin Inda Ranka na nan Freedom Radio, yana mai cewa, baza su iya daidaita farashin Shinkafa ba a yanzu domin matsalar ba daga masu samar da shinkafar bane.

Ya ƙara da cewa hana shigowa da shinkafar da gwamnatin tarayya ta yi shi ne musabbabin da ya haifar da tsadar shinkafar, kuma gwamnatocin jihohi baza su iya taɓuka komai a kai ba.

“Gwamnatin tarayya ce kaɗai zata iya kawo ƙarshen matsalar ta hanyar bada dama a ci gaba da shigo da Shinkafar kamar yadda ake shigowa da alkama” a cewar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!