Labarai
Bude boda ba yana nufin shigo da kayan da doka ta haramta ba – Kwastom
Hukumar hana fasakwauri ta Kasa shiyar Kano da Jigawa ta ce bude boda ba ya nufin a shigo da kayan da doka ta haramta ba, a don haka za sucigaba da kame duk Wani kayayyakin da aka haramata shigowa da shi kasar nan.
Shugaban hukumar Reshen Jihar Kano da Jigawa SP Umar, ya bayyana hakan ya yin taron manema labarai da ya gudana a nan Kano.
SP Umar, ya kara da cewar sun samu nasarar kame kayayyakin da suka hadar da Shinkafa da kayayyakin Gwanjo da Taliya da Maganin sauro da sauran kayayyaki da doka ta hana shigo da su kasar nan.
SP Nasir ya kuma kara da cewa mafi yawan kayan da ake fasakwauri su akwai kamfanoni da manoma dake samar dasu a nan gida Najeriya dan haka ba zasu zuba idanu a durkusar da kamfanoni da manoman Kasar nan ba.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar hana fasakwauri na gargadin masu fasakwauri tare da nema Karin hadin kai daga kafafen yada labarai wajen wayar da kan al’umma game da Illar fasakwauri.
You must be logged in to post a comment Login