Labarai
Bude kotun daukaka kara a Kano zai bunkasa harkokin shari’a- Barrister Abdul Fagge
Shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano Barrister Abdul Adamu Fagge ya bayyana cewar kaddamar da kotun daukaka kara a jIhar Kano zai kawo cigaba sosai a fannin Sharia har da bangaren tattalin arziki.
Barrister Abdul fagge ya bayyana hakan ne a Shelkwatar kungiyar lauyoyi ta Kano cikin tattaunawar su da wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail
Barrister Fagge ya kara da cewa yanzu an daina zuwa Jihar Kaduna don daukaka kara hakan sauki ne sosai ga ‘yan Sharia da lauloyi sannan mutane za su dinga zuwa Kano daga jigawa domin daukaka kara ta wani fuskar ma har bunkasa tattalin arziki zai yi.
Shugaban kungiyar lauyoyin ya kuma bayyana cewar wasu mutanen dake son daukaka kara, nesa ta zo kusa.