Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari: Babu wani mahalukin da ya isa ya durkusar da gwamnati na

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce babu wani mahaluki a kasar nan da ya isa ya durkusar da gwamnatin shugaba Buhari ko da kuwa waye shi.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.

Malam Garba Shehu ya bayyana masu ikirarin fafutukar ballewa daga kasar nan a matsayin ‘yan jagaliya da wasu ‘yan siyasa suka dauki nauyinsu, suna masu zaton cewa, hakan zai janyo fargaba ga gwamnatin shugaba Buhari.

A cewar sa babu wani mai zagon kasa ko dan kan zagin ‘yan siyasa da ya isa ya durkusar da gwamnatin shugaba Buhari, har sai wa’adin mulkinsa ya zo karshe a shekarar 2023.

Mai taimakawa shugaban kasar ya kuma ce al’ummar Nigeria ne suka zabi shugaba Buhari, saboda haka masu neman mulki ko ana ha maza ha mata da su ci gaba da jira zuwa shekarar 2023 don su gwada sa’arsu.

A baya-bayan nan ne dai wasu tsageru ciki har da tsohon shugaban tsagerun Niger Delta Asari Dokubo da shugban tsagerun matasan yarbawa Sunday Igboho suka yi barazanar fitar da yankunansu daga dunkulalliyar Nigeria.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!