Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NNPC: Mun sai da mai na tiriliyan 2 da biliyan 200 a shekarar 2020

Published

on

Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya ce tsakanin watan Disamban shekarar 2019 zuwa Disamban shekarar 2020, ya sayar da man fetur da kudinsa ya kai naira tiriliyan biyu da biliyan dari da casa’in da bakwai

Manaja mai kula da harkokin yada labarai na kamfanin na NNPC Dr. Kennie Obateru ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja.

A cewar sa wannan na cikin rahoto ne da kamfanin ya fitar game da al’amuran cinikin mai da suka faru tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020.

Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban kamfanin na NNPC na cewa an samu karin cinikin mai a watan Disamba da akalla naira biliyan ashirin da hudu da miliyan goma sha tara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!