Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zulum: Ina goyon bayan mulki ya koma kudu a 2023

Published

on

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ce akwai yarjejeniyar fahimta ta cikin gida tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke bukatar mulki ya koma kudancin kasar nan a shekarar 2023.

Gwamnan na Borno ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi wajen taron kaddamar da wani littafi da tsohon shugaban hukumar kula da gabar tekun kasar nan Dakuku Peterside ya wallafa.

Ya ce sake fasalta kasa, samar da ‘yan sandan jihohi da kuma kara ikon da jihohi suke da su duk ba zasu magance matsalolin da ke addabar kasar nan ba.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya kuma ce, akwai bukatar bai wa ‘yan Nigeria dama ana damawa da su a al’amura da dama.

Gwamnan na Borno ya ce, akwai yarjejeniyar fahimta tsakanin mambobin jam’iyyar kan komawar mulki daga yankin arewa zuwa kudu.

‘‘Na sha furta kalaman goyon bayan mulki ya koma kudancin kasar nan a shekarar 2023, kuma zan ci gaba da yin hakan har sai an cimma nasara domin hakan ne kawai zai kara hada kan al’ummar kasar nan’’ a cewar Zulum

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!