Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ga gwamnan Benue: kadaina take laifinka kana hangen na wasu

Published

on

Fadar shugaban kasa ta soki gwamnan jihar Benue Samuel Ortom sakamakon kalaman da ya furta kan rashin tsaro akan gwamnatin tarayya.

 

A ranar talata da ta gabata yayin zantawa da manema labarai, gwamnan na Benue ya zargi shugaba Buhari da yin sakaci da kuma tsara wata boyayyiyar manufa da ke neman biyan bukatun wata kabila.

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ta zargi gwmanan na Benue da cewa shi mutum ne da ke take laifinsa ya kalli na wani.

 

Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce babu wata gwamnati ta gari da za ta zura ido tana ganin ana zubar da jinin al’ummarta babu gaira babu dalili, amma shi gwamnan Benue a matsayin na babban jami’in tsaro a jihar sa wata gudunmawa ya bayar wajen dakile irin wadannan matsala.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!