Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Harin gwamnan Benue ya shafi duk dan Najeriya – Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da aka kai wa Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu na cewa, kai hari ga ko wane ɗan Najeriya tamkar kai hari ne ga al’ummar Najeriya baki-ɗaya.

Shugaba Buhari ya ce, tuni ya umarci jami’an tsaro kan su zurfafa bincike game da lamarin, kuma wannan hari ba abu ne da za a mayar da shi batun siyasa ba, a’a batu ne da ya shafi jama’ar ƙasa baki-ɗaya.

A ƙarshe shugaban ya yi alƙawarin cewa, Gwamnatinsa za ta tabbatar an yi ƙwaƙƙwaran bincike a kai, tare da ɗaukar mataki a kan duk wanda aka samu da hannu a ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!