Labarai
Jihohi sha biyar za su sami tallafin ilimi daga Global Partnership For Education – Buhari
Hukumar kula da tatalin arziki ta kasa ta ce jihohi sha biyar a kasar nan za su samu tallafin ilimi daga wata kungiyar tallafawa ilimi mai suna Global Partnership For Education a wani mataki na magance matsalar da annobar corona ta yiwa bangaren ilimi.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’I ne ya bayyana haka lokacin taron kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
An gudanar da taron ne ta kafar Internet a fadar shugaba kasa da ke Villa a Abuja.
Nasir El-rufa’I ya ce jihohin da za su samu tallafin sune jihar Abia, Anambra, Akwa Ibom, Benue, Ebonyi, Jigawa.
Sauran sun hadar:- jihar Kaduna, Katsina, Kebbi, Kano, Nassarawa, Niger, Plateau, Sokoto da kumad Zamfara.
Yace, ma’aikatar ilimi ta tarayya ta gabatawra da hukumar wasu ka’idoji da za a bi ta yadda daliban za su ci gaba da karatu a wannan yanayi na corona.
You must be logged in to post a comment Login