Connect with us

Labaran Kano

Za mu fatattaki barayin waya a yankin mu – Bakin Bulo Network For Better Tomorrow

Published

on

Kungiyar Bakin Bulo Network For Better Tomorrow ta ce ta shirya tsaf domin kare unguwar Bakin Bulo daga shigowar barayin waya da suka addabi Unguwar a ‘yan kwanakin nan da sace-sacen waya har ma da illata mutane.

Shugaban kungiyar Kwamared Muhammad Sa’id Abdullahi ne ya bayyana haka a yayin taron da kungiyar ta gudanar a Makarantar Ammar Bn Yasser Al-Islamiyya dake Unguwar.

Shugaban ya kuma ce wajibi ne mawadatan yankin su tallafawa matasan da kayan aiki da sauran bukatunsu don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A ‘yan kwanakin nan Unguwar na fama da matsalar barayi masu sace-sacen waya, inda ko a makon jiya sai da barayin suka hallaka wani matashi a unguwar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,225 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!