Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na ganawa da gwamnoni da manyan hafsoshin kasar nan

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagoraranci wani taro kan harkokin tsaro tare da kwamitin kula da harkokin tsaro na kungiyar gwamnonin kasar nan karkashin jagorancin gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Rahotanni sun ce taron ya kuma samu halartar mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Muhammad Adamu da babban hafsan tsaro na kasa janar Gabriel Olonisakin da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ibas da babban hafsan sojojin kasa laftanal janar Tukur Buratai wanda manjo janar US Yakubu ya wakilta.

Sauran sune: babban hafsan sojin sama na kasar nan Air Marshal Sadique Abubakar da daraktan hukumar leken asiri ta kasa NIA Ambasada ahmed Rufai da kuma daraktan hukumar tsaron sirri ta DSS Yusuf Bichi.

A bangaren gwamnoni kuwa wadanda suka halarci taron sun hada da: gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da na Bayelsa Sanata Duoye Diri da gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum da David Umahi na jihar Ebonyi da kuma Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!