Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mikel zai dawo taka leda a firimiyar Ingila

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles da Chelsea  mai shekaru 33, Mikel Obi  zai  dawowa kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion ta kasar Ingila akakar wasa ta badi.

Kungiyar dai ta West Brom ta samu zarafin zuwa gasar firimiyar ta bane ne bayan da ta kasance daya daga cikin kungiyoyi ukun farko daga gasar Championship sai dai har zuwa yanzu ba’a tsayar da yarjejeniya tsakanin dan wasan da kungiyar ba.

Ajiya ne Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta West Brom, Slaven Bilic ya shaidawa manema labarai a birnin Landan cewa idan Dan wasan Mikel ya amince da dawowa kungiyarsa, babu shakka kungiyar za ta taka rawar gani a gasar ta firimiyar badi.

Ya zuwa yanzu dai bayan kungiyar kwallon kafan ta West Brom babu wata kungiya da ta nuna sha’awar daukar dan wasan tun bayan da al’amuran kwallon kafa suka faro dawo dai-dai sakamakon annobar Coronavirus.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!