Connect with us

Labarai

Yanzu-yanzu Buhari na ganawar sirri da Goodluck

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan a fadar sa.

Rahotanni sun bayyana cewa har kawo yanzu ba a kai ga sanin batun da suka tattauna a tsakanin su ba, sai dai ana ganin ganawar ta su na da nasaba da batun sasanta rikicinn siyasa da ya dabaibaye kasar Mali.

Goodluck Jonathan dai daya ne daga cikin ‘yan gaba-gaba da ke kokarin ganin an kawo karshen rikicin siyasa da ya addabi kasar ta Mali.

Tun a baya dai shugabannin kasashen yammacin afrika suka shiga cikin rikicin na Mali don sasantawa, a wani mataki na inganta zaman lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,158 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!