Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin adalci a shari’a ne ke haifar da matsaloli- KCSF

Published

on

Ƙungiyar kishin al’umma ta Kano Civil Society KCSF tare da tallafin kungiyar tabbatar da doka da yaki da cin hanci da rashawa ta RoLAC sun bayyana cewa, rashin wayar da kan mutane sanin muhimmancin tabbatar da yin adalci a yayin gudanar da shari’ar manyan laifuka shi ke haifar da matsaloli na shari’a a tsakanin al’umma.

Kungiyar ta KCSF wacce cibiyar raya aladu ta Birtaniya ke aiwatar da shirye-shirye ya yin da kungiyar tarayya Turai ke daukar nauyi tace, wayar da kan al’umma ta hanyar kungiyoyi zai taimaka rawa wajen warware matsaloli a cikin a’lumma, ba tare da samun wani cikas ba.

Shugaban ƙungiyar ta kasa reshen jihar Kano Ibrahim A. Waiya ne ya bayyana hakan, lokacin buɗe taron ƙarawa juna sani na yini guda da aka yi a cibiyar wanzar da Dimukuraddiya ta Mambayya dake nan Kano.

Ibrahim Waiya ya ce, tsage gaskiya da tabbatar da adalci a lokacin da aka kama duk mai laifi shine zai kawo ci gaba a yayin gudanar da shari’a a kasar nan.

Da yake jawabi a yayin taron shugaban kungiyar RoLAC na jihar Kano Alhaji Ibrahim Bello ya ce, duk da ayyukan kungiyar yazo karshe amma sun cimma nasarori da dama wajen wayar da kan mutane idan an kama su.

Kazalika Dr, Nuhu Musa na sashin nazari kan cinikayya da tabbatar da doka na tsangayar nazarin shari’a a jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya zayyano dokokin da suka bayyana yadda za a tsare mutum a kuma kama shi.

Har ila yau, wata ƴar gwagwarmaya Barrister Maryam Ahmad ta ambato wasu dokokin shekara ta1999 da ya jibinci tsarewa da kama mai laifi.

Wakiliyar mu Hassana Salisu Abubakar ta rawaito cewa, taron wanda na yini guda ne ya sami halartar masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jiar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!