Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na neman sahalewar majalisa wajen nadin mai binciken kudi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan Mr Aghughu Adolphus ga majalisar dattijai domin tantance shi a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya.

Muhammadu Buhari ya aike da wasika ga shugaban majalisar dattijan Sanata Ahmad Lawan domin amince wa Mr Adolphus, kamar yadda sashe na 86(1) na kundin tsarin mulkin kasar nan ya yi tanadi.

Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai Sanata Babajide Omoworare ya fitar.

Sanarwar ta ce Aghughu Adolphus ya rike mukamin a matsayin rikon kwarya tun bayan ritayar da Mr Anthony Mkpe Ayine ya yi a ranar 25 ga watan Oktoban bara sakamakon cika shekaru 60 da haihuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!