Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ‘yan sanda suka tabbatar da ‘yan bindiga sun kashe jami’an su a Taraba

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ta tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’anta guda biyu a karamar hukumar Karim Lamido.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP David Misal ne ya tabbatar da hakan yau, inda ya ce ‘yan bindigar sun hallaka ‘yan sandan ne jiya litinin, bayan da motarsu ta lalace a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa aiki garin Jen da ke kan titin Karim Lamido.

Bayan kashen ‘yan sandan ne kuma sai suka yi awon gaba da bindigoginsu guda biyu suka tsere cikin daji.

Kisan ‘yan sandan na zuwa ne kwanaki uku bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe shugaban karamar hukumar Ardo-Kola ta Jihar da wani ‘dan uwansa a garin garin Jalingo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!