Labarai
Buhari ya aikewa majalisa ƙudurin ƙarin kasafin kuɗi na 2022
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya mikawa majalisar dokokin Najeriya ƙarin kudirin kasafin kuɗi na naira tiriliyan 2 da biliyan 55 domin amincewa.
Kazalika shugaba Buhari na neman a sake duba dokar kasafi ta 2022 domin samun ƙarin kasafin kuɗin tallafin man fetur daga watan Yuni zuwa Disambar 2022.
Buƙatar hakan na cikin wata wasiƙa da aka aikawa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a ranar Talata.
Buhari ya kuma buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta dawo da wasu ayyukan da majalisar ta cire tun da farko a cikin kasafin kuɗin 2022.
Idan za a iya tunawa dai tun da fari Buhari ya koka kan sauyin da ƴan majalisar suka yi a cikin ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2022 na Naira tiriliyan 17 da biliyan 126 da ya sanyawa hannu a cikin watan Disamba.
Sai dai majalisar ta amince da Naira tiriliyan 17 da biliyan 1 saɓanin Naira tiriliyan 16 da biliyan 3 da ya gabatar a watan Oktoba, inda ya ƙara kusan Naira biliyan ɗari 700 a cikin kasafin kuɗin.
You must be logged in to post a comment Login