Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya aikewa sarki Salman na Saudiyi addu’ar samun sauki

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa sarkin Salman Bin Abdulazizi na Saudiya addu’ar samun sauki cikin hanzari wanda aka kwantar a Asibiti.

Muhammadu Buhari ya ce a madadin gwamnati sa da ta ‘yan Najeriya yana yi wa Sarkin Salman addu’ar Allah ya tashi kafadon sa cikin sauri.

Sakon na kunshe ta cikin sanarwar da kakakin fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu.

Ka zalika ta cikin sanarwar Buhari ya ce Sarki Salaman na daya daga cikin shugabanin duniya mutanen kirki da ya taba haduwa da su.

Labarai masu alaka : 

Buhari ya gana da Sarki Salman

Covid-19: Sarkin Saudiya ya killace kansa

Shugaban na Najeriya ya sake nanata cewar, Sarkin Salman abokin Najeriya ne na hakika wanda bai taba nuna gazawar sa ba a bangaren hadin kasashen guda biyu ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!